Sai kuma ta sāke yin ciki, ta haifi ɗa, ta ce, “Yanzu, a wannan karo mijina zai shaƙu da ni, domin na haifa masa 'ya'ya uku maza.” Saboda haka ta raɗa masa suna Lawi.
'Ya'yan Yahuza, maza, su ne Er, da Onan, da Shela, da Feresa, da Zera, (amma Er da Onan suka rasu a ƙasar Kan'ana). 'Ya'yan Feresa, maza kuwa, su ne Hesruna da Hamul.
Waɗannan su ne shugabannin gidajen kakanninsu. 'Ya'yan Ra'ubainu, maza, ɗan farin Isra'ila, su ne Hanok, da Fallu, da Hesruna, da Karmi. Waɗannan su ne iyalan kabilar Ra'ubainu.