Yusufu ya kasa daurewa a gaban dukan waɗanda suke a tsaye kusa da shi, sai ya ta da murya ya ce, “Kowa ya ba mu wuri.” Saboda haka ba mutumin da ya tsaya a wurin sa'ad da Yusufu ya bayyana kansa ga 'yan'uwansa.
Allah ya ce, “Na daɗe na yi shiru, Ban amsa wa jama'ata ba. Amma yanzu lokaci ya yi da zan yi wani abu, Na yi ƙara kamar matar da take fama da zafin naƙuda.