Farawa 43:23 - Littafi Mai Tsarki23 Ya amsa ya ce, “Salama na tare da ku, kada ku ji tsoro, Allahnku da Allah na mahaifinku ne kaɗai ya sa muku dukiyar cikin tayakanku. Na karɓi kuɗinku.” Sai ya fito musu da Saminu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202023 Sai mai hidimar ya ce, “Ba kome, kada ku ji tsoro. Allahnku, Allahn mahaifinku ne ya ba ku dukiyar a cikin buhunanku; ni dai, na karɓi azurfanku.” Sa’an nan ya fitar musu da Simeyon. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Waɗansu sojoji daga Manassa, suka tafi wurin Dawuda sa'ad da yake fita tare da Filistiyawa don su yi yaƙi da Saul. Amma Dawuda bai tafi tare da su ba, domin sarakunan Filistiyawa sun yi shawara, suka sallame shi, don kada ya juya musu gindin baka, ya nemi sulhu a wurin shugabansu Saul, da kawunansu.