Amma da ya yi ta ja musu rai, sai mutanen suka kama hannunsa, da na matarsa, da na 'ya'yansa biyu mata, saboda jinƙan da Ubangiji ya yi masa, suka fitar da shi suka kai shi a bayan birnin.
Mahaifinsu, Isra'ila ya ce musu, “In tilas haka zai zama, sai ku yi wannan, ku ɗiba daga cikin zaɓaɓɓu, mafiya kyau na albarkar ƙasar a cikin tayakanku, ku kai wa mutumin tsaraba, da ɗan man shafawa na ƙanshi da 'yar zuma, da kayan yaji, da ƙaro, da tsabar citta, da ɓaure.