Wannan shi ne tarihin zuriyar Yakubu. Yusufu yana da shekara goma sha bakwai sa'ad da ya zama makiyayin garke tare da 'yan'uwansa, ɗan ƙanƙanen yaro ne a tsakanin 'ya'ya maza na Bilha da Zilfa matan mahaifinsa. Sai Yusufu ya kawo labarin munanan abubuwa da 'yan'uwansa suke yi a wurin mahaifinsa.
Yusufu yana da shekara talatin lokacin da ya kama aiki a wurin Fir'auna, Sarkin Masar. Yusufu kuwa ya fita daga gaban Fir'auna ya ratsa dukan ƙasar Masar.