3 Don haka 'yan'uwan Yusufu su goma suka gangara su sayo hatsi a Masar.
3 Sai goma daga cikin ’yan’uwan Yusuf suka gangara don su saya hatsi daga Masar.
Suka ce, “Mu bayinka, 'yan'uwan juna ne, mu goma sha biyu muke maza, 'ya'yan mutum guda a ƙasar Kan'ana, ga shi kuwa autanmu yana tare da mahaifinmu a yanzu, ɗayan kuwa ya rasu.”
Haka nan 'ya'yan Isra'ila maza suka zo su sayi hatsi tare da sauran matafiya, gama ana yunwa a ƙasar Kan'ana.
Ga shi kuwa, na ji akwai hatsi a Masar, ku gangara ku sayo mana hatsi a can domin mu rayu, kada mu mutu.”
Amma Yakubu bai aiki Biliyaminu ɗan'uwan Yusufu tare da 'yan'uwansa ba, gama ya ce, “Kada wata ɓarna ta same shi.”