Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 42:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Suka ce, “Mu bayinka, 'yan'uwan juna ne, mu goma sha biyu muke maza, 'ya'yan mutum guda a ƙasar Kan'ana, ga shi kuwa autanmu yana tare da mahaifinmu a yanzu, ɗayan kuwa ya rasu.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Amma suka amsa suka ce, “Bayinka dā su goma sha biyu ne, ’yan’uwa, ’ya’yan mutum guda maza, wanda yake zama a ƙasar Kan’ana. Ƙaraminmu yanzu yana tare da mahaifinmu, ɗayan kuma ya rasu.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 42:13
26 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

ya koma wurin 'yan'uwansa, ya ce, “Saurayin ba ya nan, ni kuwa, ina zan sa kaina?”


Sai muka amsa, ranka ya daɗe, muka ce, ‘Muna da mahaifi, tsoho, da ɗan tsufansa, auta, wanda ɗan'uwansa ya rasu, shi kaɗai ya ragu daga cikin mahaifiyarsa, mahaifinsa kuwa yana ƙaunarsa.’


Mu sha biyu ne 'yan'uwan juna, 'ya'ya maza na mahaifinmu, ɗayan ya rasu, autan kuwa yana tare da mahaifinmu a yanzu haka a ƙasar Kan'ana.’


Suka amsa, “Ai, mutumin ne ya yi ta tambayar labarinmu da na danginmu, yana cewa, ‘Mahaifinku yana da rai har yanzu? Kuna kuma da wani ɗan'uwa?’ Abin da muka faɗa masa amsoshi ne na waɗannan tambayoyi. Ta ƙaƙa za mu iya sani zai ce, ‘Ku zo da ɗan'uwanku’?”


“An ji wata murya a Rama, Ta kuka da baƙin ciki mai zafi, Rahila ce take kuka saboda 'ya'yanta. Ba za ta ta'azantu ba, don ba su.”


Da Hirudus ya ga masanan nan sun mai da shi wawa, sai ya hasala ƙwarai, ya aika a karkashe dukan 'yan yara maza da suke Baitalami da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, gwargwadon lokacin da ya tabbatar a gun masanan nan.


Ubanninmu sun yi zunubi, ga shi kuwa, ba su, Mu kuwa muna ɗaukar alhakin muguntarsu.


Ga abin da Ubangiji ya ce, “An ji murya daga Rama, Muryar baƙin ciki da kuka mai zafi, Rahila tana kuka saboda 'ya'yanta, ba su.


Suka ce masa, “Har yanzu Yusufu yana nan da rai, shi ne kuwa mai mulki bisa ƙasar Masar duka.” Sai gabansa ya fāɗi, domin bai gaskata su ba.


ɗayan ya bar ni, na kuwa ɗauka, hakika an yayyage shi kaca kaca, gama ban ƙara ganinsa ba.


Amma ya ce, “Ɗana ba zai gangara tare da ku ba, ga ɗan'uwansa ya rasu, shi kaɗai kuwa ya ragu. Zai yiwu a kashe shi a hanya. Na tsufa ƙwarai ba zan iya ɗaukar wannan baƙin ciki ba, zai kashe ni.”


Sai Yakubu mahaifinsu, ya ce musu, “Kun sa ni rashi, ga shi, ba Yusufu, Saminu ba shi, wai kuma yanzu za ku ɗauki Biliyaminu, ga dai irin abubuwan da suka faɗo mini.”


Mu duka 'ya'yan mutum guda ne, amintattu kuma, bayinka ba magewaya ba ne.”


Yusufu ya ce musu, “A'a! Ku dai kun zo ku ga inda ƙasarmu yake da rashin ƙarfi.”


Amma Yusufu ya ce musu, “Ai, kamar dai yadda na faɗa muku, magewaya ne ku.


Sai ya ɗaga idanunsa, ya ga ɗan'uwansa Biliyaminu, ɗan da mahaifiyarsa ta haifa, ya ce, “Wannan shi ne auta naku, wanda kuka yi mini magana a kansa? Allah ya yi maka alheri ɗana!”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ