'Yan'uwansa suka ce masa, “Ashe, lalle ne kai za ka sarauce mu? Ko kuwa, ashe lalle ne kai za ka mallake mu?” Sai suka daɗa ƙin jininsa domin mafarkansa da maganganunsa.
Ishaku ya amsa wa Isuwa ya ce, “Ga shi, na shugabantar da shi a kanka da dukan 'yan'uwansa na ba shi su, su zama barorinsa, na ba shi hatsi da ruwan inabi. Me zan yi maka kuma, ya ɗana?”
Bari jama'a su bauta maka, Al'ummai kuma su sunkuya maka. Za ka yi shugabancin 'yan'uwanka, Allah ya sa 'ya'yan mahaifiyarka su sunkuya maka. La'ananne ne dukan wanda ya la'anta ka, Albarkatacce ne dukan wanda ya sa maka albarka.”