Da ma a sami hatsi mai yawa a ƙasar, Da ma amfanin gona yă cika tuddan, Yă yi yawa kamar itatuwan al'ul na Lebanon, Da ma birane su cika da mutane, Kamar ciyayin da suke girma a sauruka.
Yusufu yana da shekara talatin lokacin da ya kama aiki a wurin Fir'auna, Sarkin Masar. Yusufu kuwa ya fita daga gaban Fir'auna ya ratsa dukan ƙasar Masar.
sai ya tattara dukan abinci na shekarun nan bakwai da aka yi na ƙoshi a ƙasar Masar, ya kuwa tanada abinci cikin birane, a kowane birni ya tanada abinci daga karkarar da take kewaye da shi.