ya kuma tsamo shi daga dukan wahala tasa, ya ba shi farin jini da hikima a gun Fir'auna, Sarkin Masar, shi kuwa ya naɗa shi mai mulkin Masar, ya kuma danƙa masa jama'ar gidansa duka.
Sai Ahab ya yi magana da Nabot ya ce, “Ka ba ni gonar inabinka don in mai da ita lambu, gama gonar tana kusa da gidana, ni kuwa zan ba ka wata gonar inabi a maimakonta, idan kuma kana so, sai in ba ka tamanin kuɗinta.”
Sa'ad da Finehas, firist, da shugabannin jama'a, wato shugabannin iyalan Isra'ila, suka ji maganar da Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa suka faɗa, suka ji daɗi a rai.