Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 41:30 - Littafi Mai Tsarki

30 amma a bayansu za a yi shekara bakwai na yunwa, amma za a manta da dukan ƙoshin nan a ƙasar Masar, yunwar kuwa za ta game dukan ƙasar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

30 amma shekaru bakwai na yunwa za su biyo bayansu. Tsananin yunwar za tă sa a manta da dukan isashen abincin da aka samu a ƙasar Masar, yunwa kuwa za tă rufe dukan ƙasar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 41:30
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A yanzu cikin ƙasar duka, ba abinci, gama yunwar ta tsananta ƙwarai, har ƙasar Masar da ƙasar Kan'ana suka matsu saboda yunwar.


aka fara shekaru bakwai na yunwa kamar yadda Yusufu ya faɗa. Sai aka yi yunwa cikin sauran ƙasashe duka, amma a ƙasar Masar akwai abinci.


Iliya ɗan adam ne kamarmu, amma da ya nace da addu'a kada a yi ruwa, sai da aka shekara uku da wata shida ba a yi ruwa a ƙasar ba.


Sa'ad da Ubangiji ya aukar da yunwa a ƙasarsu, Ya kuma sa abincinsu duka ya ƙare,


Amma gaskiya nake gaya muku, a zamanin Iliya akwai mata gwauraye da yawa a Isra'ila, wato a lokacin da aka hana ruwan sama har shekara uku da wata shida, sa'ad da babbar yunwa ta game dukan ƙasar.


Dukan wanda yake so ya roƙi albarka, sai ya roƙi Allah ya sa masa albarka, Allah da yake mai aminci ne. Dukan wanda zai sha rantsuwa, sai ya rantse da sunan Allah, Allah da yake mai aminci ne. Wahalan dā za su ƙare, za a kuwa manta da su.”


Bari ya sha don ya manta da talaucinsa, don kada kuma ya ƙara tunawa da ɓacin ransa.


Elisha kuwa ya ce wa matar da ya ta da ɗanta daga matattu, “Ki tashi, ke da gidanki, ki zauna duk inda kika samu, gama Ubangiji ya sa a yi yunwa a ƙasar har shekara bakwai.”


Wani annabi mai suna Iliya, mutumin Tishbi a Gileyad, ya ce wa sarki Ahab, “Na rantse da Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda nake bauta wa, ba za a yi raɓa ko ruwan sama cikin shekarun nan ba, sai da faɗata.”


Sai Gad ya zo wurin Dawuda ya ce masa, “Kana so a yi yunwa shekara uku a ƙasarka? Ko kuwa kana so ka yi ta gudu a gaban abokan gabanka har wata uku? Ko kuwa ka fi so a yi annoba kwana uku a ƙasarka? Yanzu sai ka yi tunani, ka faɗi irin amsar da zan mayar wa Ubangiji da ya aiko ni.”


Domin haka sa'ad da yunwar ta bazu ko'ina a ƙasar, Yusufu ya buɗe taskokin ajiya, ya yi ta sayar wa Masarawa, gama yunwa ta tsananta a ƙasar.


Yusufu ya raɗa wa ɗan farin suna, Manassa, yana cewa, “Gama Allah ya sa ni in manta da dukan wahalata da dukan gidan mahaifina.”


Ramammun shanun nan bakwai da suka fito a bayansu shekaru bakwai ne, busassun zangarkun nan bakwai waɗanda iskar gabas ta ƙeƙasar kuwa, shekaru bakwai ne na yunwa.


amma da suka haɗiye su, ba wanda zai iya sani sun haɗiye su, gama suna nan a ramammunsu kamar yadda suke a dā. Sai na farka.


Zai kuwa zama kamar ba a taɓa yin ƙoshi a ƙasar ba, saboda tsananin yunwar.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ