Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 41:23 - Littafi Mai Tsarki

23 zangarku bakwai kuma busassu sirara waɗanda iskar gabas ta ƙeƙasar, suka fito a bayansu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Bayansu, sai ga waɗansu kawuna bakwai suka fito, yanƙwananne sirara waɗanda iskar gabas ta yanƙwane.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 41:23
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ko da yake Isra'ila tana bunƙasa kamar ciyayi, Iskar gabas, wato iskar da za ta zo daga jeji, Za ta busar da maɓuɓɓugarsu da idon ruwansu, Za ta lalatar da abubuwa masu amfani da yake cikin taskarsu.


An ka da mutanen Ifraimu, saiwarsu ta bushe. Ba za su yi 'ya'ya ba. Ko ma sun haihu, zan kashe 'ya'yan nan nasu waɗanda suke ƙauna.”


Gama sun shuka iska Don haka zu su girbe guguwa. Hatsin da yake tsaye ba shi da zangarniya, Ba zai yi tsaba ba. Ko da ya yi tsaba ma, baƙi ne za su ci,


Mazauna cikinsu suka rasa ƙarfi, suka damu, suka ruɗe. Suka zama kamar ciyawar saura, ko kuma ciyawar da ta tsiro a rufin soro, da iskar gabas mai zafi ta busa, har ta bushe.


Ga shi kuma, a bayansu waɗansu zangarku bakwai suka fito sirara waɗanda iskar gabas ta ƙeƙasar.


Har yanzu kuma, a cikin mafarkina ga zangarku masu kauri kyawawa guda bakwai, suna girma a kara guda,


Siraran zangarkun kuwa suka haɗiye zangarkun nan bakwai kyawawa masu kauri. Na faɗa wa bokaye, amma ba wanda ya iya yi mini fassararsa.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ