Ni Daniyel kuwa na siƙe, na yi ciwo, har na kwanta 'yan kwanaki, sa'an nan na tashi na ci gaba da aikin sarki. Wahayin ya shige mini duhu, ban gane shi ba.
Saboda haka da safe, hankalinsa ya tashi, sai ya aika aka kirawo dukan bokayen Masar da dukan masu hikimar Masar, Fir'auna kuwa ya faɗa musu mafarkansa, amma ba wanda ya iya fassara masa su.
Suka ce masa, “Mafarkai muka yi, ba kuma wanda zai fassara mana su.” Sai Yusufu ya ce musu, “Ashe, ba a wurin Allah fassarori suke ba? Ku faɗa mini su, ina roƙonku.”
Suka yi mafarki, su biyu ɗin, a dare ɗaya, da shi mai shayarwar da mai tuyar na gidan Sarkin Masar, waɗanda aka sa a kurkuku, kowanne kuwa da nasa mafarkin da kuma tasa irin fassarar mafarkin.