Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 40:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Ya komar da shugaban masu shayarwa a matsayinsa na shayarwa, ya kuwa miƙa finjali a hannun Fir'auna,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Ya mai da shugaban masu shayarwa a matsayinsa, saboda haka shugaban masu shayarwa ya sāke sa kwaf a hannun Fir’auna,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 40:21
6 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

bayan kwana uku Fir'auna zai ɗaukaka ka, ya komar da kai matsayinka, za ka kuma sa finjalin Fir'auna a hannunsa kamar dā lokacin da kake mai hidimar shayarwarsa.


Ni kuwa ina riƙe da finjalin sarki. Wata rana a watan Nisan, a shekara ta ashirin ta sarautar sarki Artashate, sa'ad da na kai masa ruwan inabi, sai na ɗauki ruwan inabin, na ba shi. Ni ban taɓa ɓata fuskata a gabansa a dā ba, sai wannan karo.


Fir'auna ya yi fushi da ma'aikatan nan nasa biyu, wato shugaban masu shayarwa da shugaban masu tuya.


Yadda ya fassara mana haka kuwa ya zama, aka komar da ni matsayina, mai tuya kuwa aka rataye shi.”


Ya Ubangiji, ka kasa kunne ga addu'ar bawanka, da addu'o'in bayinka, waɗanda suke jin daɗin girmama sunanka. Ka ba bawanka nasara yau ka sa ya sami tagomashi a gaban mutumin nan.”


Har kafin faɗar da ya yi, ta cika. Maganar Ubangiji ta tabbatar da gaskiyar abin da ya faɗa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ