A kwandon da yake bisa ɗin akwai toye-toye iri iri domin Fir'auna, amma ga tsuntsaye suna ta ci daga cikin kwandon da yake bisa duka, wato wanda yake bisa kaina ɗin.”
Akwai wani Ba'ibrane, ɗan saurayi, tare da mu, bawan shugaban masu tsaron fāda, sa'ad da muka faɗa masa sai ya fassara mana mafarkanmu, ya yi wa kowannenmu fassara bisa kan mafarkinsa.