Waɗansu manyan ƙanƙara kuma kamar kayan jaki suka faɗo a kan mutane daga sama, har mutane suka zagi Allah, saboda bala'in ƙanƙarar. Bala'in nan da matuƙar bantsoro yake!
Ga shi, yanzu ka kore ni a guje daga fuskar ƙasar, zan zama a ɓoye daga fuskarka, zan kuma zama mai yawo barkatai, mai kai da kawowa a duniya, duk wanda ya same ni kuwa zai kashe ni.”