Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 38:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Har yanzu kuma ta sāke haihuwar ɗa, ta raɗa masa suna Shela. A Kezib ta haifi Shela.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Ta kuma haifi wani ɗa har yanzu, aka kuwa ba shi suna Shela. A Kezib ne ta haife shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 38:5
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sauran 'ya'yansa bisa ga iyalansu su ne, Shela, da Feresa, da Zera,


'Ya'yan Shela, maza, ɗan Yahuza, su ne Er wanda ya kafa garin Leka, da La'ada wanda ya kafa garin Maresha, da iyalan gidan masu aikin lilin da suke zaune a Bet-ashbeya,


'Ya'yan Yahuza, maza, su ne Er, da Onan, da Shela, da Feresa, da Zera, (amma Er da Onan suka rasu a ƙasar Kan'ana). 'Ya'yan Feresa, maza kuwa, su ne Hesruna da Hamul.


Sai Yahuza ya shaida su, ya ce, “Ta fi ni gaskiya, tun da yake ban ba da ita ga ɗana Shela ba.” Daga nan bai ƙara kwana da ita ba.


Yahuza kuwa ya ce wa Tamar surukarsa, “Yi zaman gwauranci a gidan mahaifinki, har ɗana Shela ya yi girma,” gama yana jin tsoro kada shi kuma ya mutu kamar 'yan'uwansa. Saboda haka Tamar ta tafi ta zauna a gidan mahaifinta.


Yahuza kuwa ya auro wa ɗan farinsa, Er, mata, sunanta Tamar.


Kabilar Yahuza ke nan, (Er, da Onan, 'ya'yan Yahuza sun mutu a ƙasar Kan'ana).


'Ya'yan Yahuza, maza, su ne Er, da Onan, da Shela. Waɗannan uku Batshuwa Bakan'aniya, ita ce ta haifa masa su. Amma Er, ɗan farin Yahuza, mugu ne a gaban Ubangiji, don haka Ubangiji ya kashe shi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ