'Ya'yan Yahuza, maza, su ne Er, da Onan, da Shela, da Feresa, da Zera, (amma Er da Onan suka rasu a ƙasar Kan'ana). 'Ya'yan Feresa, maza kuwa, su ne Hesruna da Hamul.
'Ya'yan Yahuza, maza, su ne Er, da Onan, da Shela. Waɗannan uku Batshuwa Bakan'aniya, ita ce ta haifa masa su. Amma Er, ɗan farin Yahuza, mugu ne a gaban Ubangiji, don haka Ubangiji ya kashe shi.