Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 38:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Ya amsa, ya ce, “Zan aiko miki da ɗan akuya daga cikin garken.” Ta ce, “Ko ka ba ni jingina, kafin ka aiko?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Ya ce, “Zan aika miki da ɗan akuya daga garkena.” Sai ta ce, “Za ka ba ni wani abu jingina, kafin ka aika da shi?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 38:17
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Maza sukan ba dukan karuwai kuɗi, amma ke ce mai ba kwartayenki kuɗi, kina ba su kuɗi don su zo wurinki don kwartanci daga ko'ina.


Sa'ad da Yahuza ya aika da ɗan akuya ta hannun abokinsa Ba'adullame don ya karɓi jinginar daga hannun matar, bai same ta ba.


Sai maigidan ya yaba wa wakilin nan marar gaskiya saboda wayonsa. Don 'yan zamani a ma'ammalarsu da mutanen zamaninsu, sun fi mutanen haske wayo.


Sai wawa kaɗai yake ɗaukar lamunin biyan basusuwan da baƙo ya ci, ya kamata a karɓi dukiyarsa jingina.


Sai ya je wurinta a gefen hanyar, ya ce, “Zo, mu kwana mana,” gama bai san ita surukarsa ba ce. Sai ta ce, “Me za ka ba ni, da za ka kwana da ni?”


Ya ce, “Wane alkawari zan yi miki?” Ta amsa, ta ce, “Ba ni hatiminka da ɗamararka da sandan da yake a hannunka.” Ya kuwa ba ta su, ya kwana da ita. Sai ta yi ciki.


Bayan 'yan kwanaki, sai Samson ya tafi ya ziyarci matarsa, ya kai mata ɗan akuya, a lokacin girbin alkama. Ya ce wa mahaifinta, “Zan shiga wurin matata a ɗakin kwana.” Amma mahaifinta bai yardar masa ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ