Yahuza ya je wurin Yusufu ya ce, “Ya shugabana, ina roƙonka, ka bar bawanka ya yi magana a kunnuwanka, kada kuma ka bar fushinka ya yi ƙuna bisa bawanka, gama daidai da Fir'auna kake.
Da Yotam ya ji wannan sai ya tafi, ya tsaya a kan Dutsen Gerizim, da babbar murya, ya ce musu, “Ku kasa kunne gare ni ku mutanen Shekem, domin kuma Allah ya kasa kunne gare ku!