Gama mutanen Ammon da na Mowab suka tasar wa mazaunan Dutsen Seyir, suka hallaka su ƙaƙaf. Sa'ad da suka karkashe mazaunan Seyir sai suka fāɗa wa juna, suka yi ta hallaka kansu da kansu.
“Yanzu kuma ga mutanen Ammon, da na Mowab, da na Dutsen Seyir, waɗanda ka hana Isra'ilawa su kai musu yaƙi sa'ad da suka fito daga ƙasar Masar, su ne mutanen da Isra'ila suka ƙyale, ba su hallaka su ba.
Waɗansu daga cikinsu, mutum ɗari biyar daga zuriyar Saminu, suka tafi wajen gabashin Edom. Waɗanda suka shugabance su kuwa, su ne 'ya'yan Ishi, wato Felatiya, da Neyariya, da Refaya, da Uzziyel.
daidai kamar yadda Ubangiji ya yi wa zuriyar Isuwa waɗanda suka zauna a Seyir, sa'ad da ya hallakar da Horiyawa a gabansu. Su kuma suka kore su suka zauna a wurinsu har wa yau.
Haka kuma Yahudawan da suke a Mowab, da Ammon, da Edom, da kuma sauran ƙasashe suka ji, cewa Sarkin Babila ya bar waɗansu mutane a Yahuza, ya kuma shugabantar da Gedaliya ɗan Ahikam, jikan Shafan a kansu,
Sa'ad da Saul ya ci sarautar Isra'ila, ya yi yaƙi da dukan abokan gābansa da suke kewaye da shi. Ya yi yaƙi da Mowabawa da Ammonawa, da Edomawa, da sarakunan Zoba, da Filistiyawa. Duk inda ya yi yaƙi ya sami nasara.
Annabcin Obadiya ke nan. Wannan shi ne abin da Ubangiji Allah ya ce a kan al'ummar Edom. Ubangiji ya aiki manzonsa wurin sauran al'umma, Mun kuwa ji saƙonsa cewa, “Ku zo! Mu tafi mu yi yaƙi da Edom!”
Girmankanki ya yaudare ki, Kina zaune a kagara, a kan dutse, Wurin zamanki yana can ƙwanƙolin duwatsu. Don haka a zuciya kike cewa, ‘Wa zai saukar da ni ƙasa?’