36 Da Hadad ya rasu, sai Samla na Masreka ya ci sarauta a bayansa.
36 Sa’ad da Hadad ya rasu, Samla daga Masreka ya gāje shi.
Da Husham ya rasu, sai Hadad ɗan Bedad wanda ya ci Madayana a ƙasar Mowab, ya ci sarauta a bayansa, sunan birninsa kuwa Awit ne.
Da Samla ya rasu, sai Shawul na Rehobot ta Yufiretis ya ci sarauta a bayansa.