Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Oholibama matar Isuwa, shugaba Yewush, da Yalam, da Kora, waɗannan su ne shugabanni waɗanda Oholibama matar Isuwa, 'yar Ana ta haifa.
Sa'ad da Saul ya ci sarautar Isra'ila, ya yi yaƙi da dukan abokan gābansa da suke kewaye da shi. Ya yi yaƙi da Mowabawa da Ammonawa, da Edomawa, da sarakunan Zoba, da Filistiyawa. Duk inda ya yi yaƙi ya sami nasara.