11 'Ya'yan Elifaz su ne Teman, da Omar, da Zeho, da Gatam, da Kenaz.
11 ’Ya’yan Elifaz maza su ne, Teman, Omar, Zefo, Gatam da Kenaz.
Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Isuwa, maza, wato Elifaz ɗan Ada matar Isuwa, Reyuwel ɗan Basemat matar Isuwa.
Timna kuwa ƙwarƙwarar Elifaz ɗan Isuwa ce, ta haifa wa Elifaz Amalek. Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Ada, matar Isuwa.
Sa'ad da uku daga cikin abokan Ayuba, wato Elifaz daga birnin Teman, da Bildad daga ƙasar Shuwa, da Zofar daga ƙasar Na'ama, suka ji labarin irin yawan wahalar da Ayuba yake sha, sai suka kama hanya suka tafi su ziyarce shi, su ta'azantar da shi.
Ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya faɗa a kan Edom, “Ba hikima kuma a cikin Teman? Shawara ta lalace a wurin masu basira? Hikima ta lalace ne?
Jarumawanka za su firgita, ya Teman, Za a kashe kowane mutum daga dutsen Isuwa.