Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 35:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Saboda haka, suka bai wa Yakubu dukan gumakan da suke da su, da zobban kunnuwansu. Sai Yakubu ya ɓoye su a ƙarƙashin itacen oak wanda suke kusa da Shekem.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Saboda haka suka ba Yaƙub dukan baƙin allolin da suke da su, da zoban da suke kunnuwansu, sai Yaƙub ya binne su a ƙarƙashin itacen oak a Shekem.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 35:4
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai shugabannin Shekem duka da na Betmillo suka taru suka naɗa Abimelek sarki kusa da itacen oak na al'amudin da yake a Shekem.


Za ku kwashe gumakanku waɗanda aka dalaye da azurfa, da waɗanda aka rufe da zinariya, ku jefar da su kamar abin ƙyama, kuna ihu, kuna cewa, “Ku ɓace mana da gani!”


Sai ku ƙone siffofin gumakansu. Kada ku yi ƙyashin azurfa ko zinariya da aka dalaye su da ita. Kada ku kwashe su, don kada su zamar muku tarko, gama Ubangiji Allahnku yana ƙyamarsu.


Ya ɗauki siffar ɗan maraƙin da suka yi, ya ƙone ta, ya niƙe, ta zama gari, ya barbaɗa a ruwa, ya sa Isra'ilawa su sha.


Zan hukunta ta saboda kwanakin idodin gunkin nan Ba'al. A kwanakin nan takan ƙona musu turare, Ta yi ado da zobe da lu'ulu'ai, Ta bi samarinta, amma ta manta da ni.” In ji Ubangiji.


Sa'ad da wannan rana ta yi za su zubar da gumakan da suka yi na zinariya da azurfa, za su bar wa ɓeraye da jemagu.


Ga yadda za ku yi da su, za ku rurrushe bagadansu, ku ragargaza al'amudansu, ku sassare ginshiƙansu na tsafi, ku ƙaƙƙone sassaƙaƙƙun siffofinsu.


Abram ya ratsa ƙasar zuwa Shekem, wurin itacen oak na More. A lokacin nan Kan'aniyawa suke a ƙasar.


sa'an nan mu tashi mu haura zuwa Betel, domin in kafa bagade ga Allah wanda ya taimake ni a kwanakin ƙuncina, wanda kuwa yake tare da ni duk inda na tafi.”


Da suna cikin tafiya, razana daga Allah ta fāɗa wa biranen da suke kewaye da su, har ba wanda ya iya bin 'ya'yan Yakubu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ