Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 35:3 - Littafi Mai Tsarki

3 sa'an nan mu tashi mu haura zuwa Betel, domin in kafa bagade ga Allah wanda ya taimake ni a kwanakin ƙuncina, wanda kuwa yake tare da ni duk inda na tafi.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Sa’an nan ku zo, mu haura zuwa Betel, inda zan gina bagade wa Allah wanda ya amsa mini a ranar wahalata, wanda kuma ya kasance tare da ni a dukan inda na tafi.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 35:3
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'ad da kuke bi ta cikin ruwa mai zurfi, Zan kasance tare da ku, Wahala ba za ta fi ƙarfinku ba. Sa'ad da kuke bi ta cikin wuta, ba za ku ƙuna ba, Wuyar da ta same ku ba za ta cuce ku ba.


Yakubu fa ya tsorata ƙwarai, ya damu, sai ya karkasa mutanen da suke tare da shi, da garkunan tumaki da awaki, da na shanu, da raƙuma cikin ƙungiya biyu,


Ubangiji ya ce wa Yakubu, “Ka koma ƙasar kakanninka da danginka, ni kuwa ina tare da kai.”


A cikin dukan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, shi kuma zai nuna maka hanyar da take daidai.


Da ba domin Allah na mahaifina da Ibrahim, da martabar Ishaku na wajena ba, hakika da yanzu ka sallame ni hannu wofi. Allah ya ga wahalata da aikin hannuwana, ya kuwa tsauta maka a daren jiya.”


Ku jama'ar da suke zaune a Urushalima ba za ku ƙara yin kuka ba. Ubangiji mai juyayi ne, sa'ad da kuka yi kuka gare shi neman taimako, zai amsa muku.


Cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji, Ya kuwa cece su daga wahalarsu.


Ku yi kira gare ni sa'ad da wahala ta zo, Zan cece ku, Ku kuwa za ku yabe ni.”


Aka bar Yakubu shi kaɗai. Sai wani mutum ya kama shi da kokawa har wayewar gari.


Ga shi, ina tare da kai, zan kiyaye ka duk inda ka tafi, zan kuwa komo da kai ƙasan nan, gama ba zan rabu da kai ba, sai na aikata abin nan da na hurta maka.”


Dole ne su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa, Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu!


Sa'ad da suka kira gare ni, zan amsa musu, Zan kasance tare da su sa'ad da suke shan wahala, Zan cece su in girmama su.


Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, Kullum a shirye yake yă yi taimako a lokacin wahala.


Saboda haka, suka bai wa Yakubu dukan gumakan da suke da su, da zobban kunnuwansu. Sai Yakubu ya ɓoye su a ƙarƙashin itacen oak wanda suke kusa da Shekem.


A nan ya gina bagade, ya sa wa wurin suna El-betel, domin a nan Allah ya bayyana kansa gare shi sa'ad da yake guje wa ɗan'uwansa.


Sa'ad da ka wuce nan, ka ci gaba zuwa itacen oak a Tabor, a nan mutum uku da suke haurawa zuwa ɗakin Allah a Betel za su gamu da kai. Ɗaya yana ɗauke da 'yan awaki uku, ɗaya kuma yana ɗauke da malmalar abinci guda uku, ɗayan kuwa yana ɗauke da salkar ruwan inabi.


Sai ya sa wa Yusufu albarka, ya ce, “Allah na Ibrahim da Ishaku, Iyayena da suka yi tafiyarsu a gabansa, Allah da ya bi da ni Dukan raina har wa yau, ya sa musu albarka.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ