Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 34:7 - Littafi Mai Tsarki

7 'Ya'yan Yakubu, maza, kuwa sa'ad da suka komo daga saura, da suka ji yadda aka yi, sai suka hasala, abin ya ba su haushi ƙwarai, don Shekem ya yi aikin wauta ga Isra'ila da ya kwana da 'yar Yakubu. Gama irin wannan abu, bai kamata a yi shi ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Da ’ya’yan Yaƙub maza suka dawo daga jeji sai suka ji labarin. Abin kuwa ya zafe su ƙwarai, don Shekem ya jawo abin kunya wa jama’ar Isra’ila ta wurin kwana da ’yar Yaƙub, don bai kamata wannan abu yă faru ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 34:7
27 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ni kuwa na ɗauki gawarta na yanyanka gunduwa gunduwa na aika cikin ƙasar gādon Isra'ila duka, gama waɗannan mutane sun aikata abin ƙyama da abin kunya ga dukan Isra'ila.


Zai zama kuwa wanda aka same shi da haramtattun abubuwa, za a ƙone shi da wuta, shi da dukan abin da yake da shi, domin ya tā da alkawarin Ubangiji, ya kuma yi abin kunya cikin Isra'ila.’ ”


sai a kai yarinyar a ƙofar gidan mahaifinta, sa'an nan mutanen garin su jajjefe ta da duwatsu har ta mutu, don ta yi aikin wauta cikin Isra'ila, gama ta yi karuwanci a gidan mahaifinta. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.


Kowa yă girmama aure, Gădon aure kuwa yă zauna marar dauɗa, don fasikai da mazinata Allah zai hukunta su,


Abimelek kuwa ya kira Ibrahim, ya ce masa, “Me ke nan ka yi mana? Wane laifi na yi maka, da za ka jawo bala'i mai girma haka a kaina da mulkina? Ka yi mini abin da bai kamata a yi ba.”


Amma ku kabila ce zaɓaɓɓiya, ƙungiyar firistocin babban Sarki, tsattsarkar al'umma, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wannan da ya kirawo ku daga cikin duhu, kuka shiga maɗaukakin haskensa.


Da baki ɗaya ake yabo, ake kuma zagi. 'Yan'uwana, ai, wannan bai kamata ba!


Kada ma a ko ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata ko kwaɗayi a tsakaninku, domin kuwa bai dace da tsarkaka ba.


Kada fa mu yi fasikanci yadda waɗansunsu suka yi, har mutum dubu ashirin da uku suka zuba a rana ɗaya tak.


Ku guji fasikanci. Duk sauran zunubin da mutum yake yi bai shafi jikinsa ba, amma mai yin fasikanci, yana ɗaukar alhalin jikinsa ne.


sai na ga waɗansu samari masu yawa waɗanda ba su gogu da duniya ba, musamman sai na lura da wani dolo a cikinsu.


Dokokinka dawwamammu ne, ya Ubangiji, Haikalinka kuwa tsattsarka ne ƙwarai, Har abada abadin.


Da Dawuda sarki ya ji wannan, sai ya husata ƙwarai.


“Kada Isra'ilawa mata da maza su shiga ƙungiyar karuwanci na addini.


In wani daga cikin talakawa ya yi zunubi, ba da gangan ba, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, to, ya yi laifi.


Idan taron jama'ar Isra'ila sun yi zunubi, ba da gangan ba, har sun aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, amma ba su farga da laifinsu ba, duk da haka sun yi laifi.


ya faɗa wa mutanen Isra'ila, in wani ya yi zunubi, ba da gangan ba, har ya karya ɗaya daga cikin dokokin Ubangiji, sai ya bi ka'idodin nan.


'ya'yansa maza da jikokinsa maza tare da shi, 'ya'yansa mata, da jikokinsa mata, ya kawo zuriyarsa dukka zuwa ƙasar Masar.


Banda haka kuma sukan koyi zaman banza, suna zirga-zirga gida gida. Ba ma kawai masu zaman banza za su zama ba, har ma sai su zama matsegunta, masu shishigi, suna faɗar abin da bai kamata ba.


Saboda haka, sai ku kashe zukatanku ga sha'awace-sha'wacen duniya, wato fasikanci, da aikin lalata, da muguwar sha'awa, da mummunan buri, da kuma kwaɗayi, wanda shi ma bautar gumaka ne.


Sai Hamor mahaifin Shekem ya fita ya je wurin Yakubu, ya yi magana da shi.


Amma Hamor ya yi magana da su, ya ce, “Zuciyar ɗana Shekem tana begen 'yarku, ina roƙonku, ku ba shi ita aure.


“Idan aka tabbatar zargin gaskiya ne, ba a kuma ga shaidar budurcinta ba,


Gama sun yi wauta a Isra'ila, sun yi zina da matan maƙwabtansu, sun yi ƙarya da sunana, ni kuwa ban umarce su ba. Ni na sani, ni ne kuma shaida, ni Ubangiji na faɗa.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ