'Ya'yan Yakubu, maza, kuwa sa'ad da suka komo daga saura, da suka ji yadda aka yi, sai suka hasala, abin ya ba su haushi ƙwarai, don Shekem ya yi aikin wauta ga Isra'ila da ya kwana da 'yar Yakubu. Gama irin wannan abu, bai kamata a yi shi ba.
Ga'al, ɗan Ebed, ya ce, “Wane ne Abimelek har mu mutanen Shekem za mu bauta masa? Ashe, ba Yerubba'al ne mahaifinsa ba, Zebul kuma shugaban yaƙinsa? Don me za mu bauta masa? Ku yi aminci ga kakanku Hamor, tushen kabilarku!