La'ananne ne fushinsu domin mai tsanani ne, Da hasalarsu kuma, gama bala'i ce. Zan warwatsa su cikin dukan ƙasar Yakubu, In ɗaiɗaitar su su cikin Isra'ilawa.
Sai Yakubu ya ce wa Saminu da Lawi, “Kun jawo mini wahala. Kun sa na zama abin ƙi ga Kan'aniyawa da Ferizziyawa mazaunan ƙasar. Mutanena kima ne, in suka haɗa kai suka fāɗa mini, za su hallaka ni, da ni da gidana.”
Allah ya ce wa Yakubu, “Tashi, ka hau zuwa Betel, ka zauna can. Can za ka gina bagade ga Allah wanda ya bayyana gare ka sa'ad da kake guje wa ɗan'uwanka Isuwa.”