Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 33:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Amma Isuwa ya ce, “Ina da abin da ya ishe ni, ɗan'uwana, riƙe abin da kake da shi don kanka.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Amma Isuwa ya ce, “Na riga na sami abin da ya ishe ni, ɗan’uwana. Riƙe abin da kake da shi don kanka.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 33:9
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Ishaku mahaifinsa ya amsa masa ya ce, “Ga shi, ni'imar ƙasar za ta nisanci mazauninka, Raɓar samaniya can ƙwanƙoli za ta nisance ka.


Na yi farin ciki ƙwarai, zuciyata kuma ta ƙarfafa saboda ƙaunar da kake yi, yă kai 'dan'uwana, domin zukatan tsarkaka sun wartsake ta dalilinka.


ba kuma a kan bawa ba, sai dai a kan abin da ya fi bawa, wato 'dan'uwa abin ƙauna, tun ba ma a gare ni ba, balle fa a gare ka, ta wajen al'amarin jiki da kuma wajen al'amarin Ubangiji.


Su kuwa da suka ji haka, suka ɗaukaka Allah. Suka ce wa Bulus, “To, kā gani ɗan'uwa, dubban mutane sun ba da gaskiya a cikin Yahudawa, dukansu kuwa masu himma ne wajen bin Shari'a.


Sai Hananiya ya tafi, ya shiga gidan. Da ya ɗora masa hannu, ya ce, “Ya ɗan'uwana Shawulu, Ubangiji ne ya aiko ni, wato Yesu, wanda ya bayyana a gare ka a kan hanyar da ka biyo, domin ka sāke gani, a kuma cika ka da Ruhu Mai Tsarki.”


mutumin da ba shi da kowa, ba ɗa, ba ɗan'uwa, duk da haka a kullum yana ta fama da aiki. Bai taɓa ƙoshi da wadatar da yake da ita ba. Saboda me yana ta fama da aiki, ya hana wa kansa jin daɗi? Wannan ma aikin banza ne, zaman baƙin cikin ne.


Lokacin da ka yi abin da Ubangiji yake so, ka iya mai da maƙiyanka su zama abokai.


Isuwa dai ya ƙi jinin Yakubu saboda albarkar da mahaifinsa ya sa masa. Sai Isuwa ya ce a ransa, “Kwanakin makoki domin mahaifina suna gabatowa, sa'an nan zan kashe Yakubu ɗan'uwana.”


Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina Habila ɗan'uwanka?” Ya ce, “Ban sani ba, ni makiyayin ɗan'uwana ne?”


Matsattsaku tana da 'ya'ya mata biyu, ana kiransu, “Ba ni, Ba ni.” Akwai abu uku da ba su ƙoshi, i, har huɗu ma da ba su cewa, “Ya isa,” wato, lahira, macen da ba ta haihuwa, ƙasa wadda ba ta ƙoshi da ruwa, wuta wadda ba ta cewa, “Ya isa.”


Ta wurin takobinka za ka rayu Za ka yi wa ɗan'uwanka barantaka, Amma sa'ad da ka ɓalle, Za ka kakkarye karkiyarsa daga wuyanka.”


Yakubu ya ce, “A'a, ina roƙonka, in dai na sami tagomashi a idonka, to, sai ka karɓi kyautar da yake hannuna, gama hakika ganin fuskarka, kamar ganin fuskar Allah ne, bisa ga yadda ka karɓe ni.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ