Sai Isuwa ya ce, “Bari in bar waɗansu daga cikin mutanen da suke tare da ni, a wurinka.” Amma Yakubu ya ce, “Ka kyauta ƙwarai, amma ba na bukatar haka, ya shugaba.”
Shugabannin Filistiyawa, su biyar suka je wurinta suka ce mata, “Ki yi masa kirsa, don ki san dalilin irin ƙarfin nan nasa, da kuma yadda za mu yi maganinsa, mu ɗaure shi don mu rinjaye shi. Kowannenmu zai ba ki shekel dubu da ɗari (1,100).”