Ina roƙonka, ka karɓi kyautar da na kawo maka, gama Allah ya yi mini alheri matuƙa, gama ina da abin da ya ishe ni.” Da haka Yakubu ya i masa, Isuwa kuwa ya karɓa.
Amma Yakubu ya ce masa, “Shugabana, ai, ka sani 'ya'yan ba su da ƙarfi, ga kuma bisashe da shanun tatsa, ina jin tausayinsu ƙwarai da gaske. Idan kuwa aka tsananta korarsu kwana ɗaya, garkunan za su mutu duka.