Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 33:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Ina roƙonka, ka karɓi kyautar da na kawo maka, gama Allah ya yi mini alheri matuƙa, gama ina da abin da ya ishe ni.” Da haka Yakubu ya i masa, Isuwa kuwa ya karɓa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Ina roƙonka ka karɓi kyautar da aka kawo maka, gama Allah ya yi mini alheri kuma ina da kome da nake bukata.” Ganin yadda Yaƙub ya nace, sai Isuwa ya karɓa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 33:11
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

An biya ni sarai, har fi. Bukatata ta biya, da na karɓi kyautar da kuka aiko mini ta hannun Abafaroditas, baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai.


Idan ka yarda ka karɓi kyautan nan da baiwarka ta kawo maka domin a ba samarin da suke tare da kai.


Na'aman kuwa ya ce, “In ka yarda ka karɓi talanti biyu na azurfa.” Ya ƙirga su ya ɗaure kashi biyu, da kuma rigunan ado masu kyau ya ɗora wa barorinsa biyu, ya umarce su su kai wa Gehazi har gida.


Amma Isuwa ya ce, “Ina da abin da ya ishe ni, ɗan'uwana, riƙe abin da kake da shi don kanka.”


Ta haka mutumin ya zama riƙaƙƙen mai arziki, yana da manya manyan garkuna da barori mata da maza, da raƙuma, da jakuna.


Horon jiki yana da ɗan amfaninsa, amma bin Allah yana da amfani ta kowace hanya, da yake shi ne da alkawarin rai na a yanzu da na nan gaba.


kamar muna baƙin ciki, kullum kuwa farin ciki muke yi, kamar matalauta muke, duk da haka kuwa muna arzuta mutane da yawa, kamar ba mu da kome, alhali kuwa kome namu ne.


Saboda haka kada kowa yă yi fariya da 'yan adam. Don kuwa kome naku ne,


Sai ubangijin biki ya ce wa bawan, ‘Fita, ka bi gwadabe-gwadabe da hanyoyin karkara, ka rinjayi mutane su shigo, don a cika gidana.


Amma suka matsa masa har suka i masa, sai ya yardar musu su tafi. Su kuwa suka tafi su hamsin. Suka yi ta neman Iliya, har kwana uku, amma ba su same shi ba.


Sa'ad da Dawuda ya komo Ziklag, sai ya aika wa abokansa, dattawan Yahuza, da rabo daga cikin ganimar, ya ce, “Ga kyauta dominku, daga cikin ganimar maƙiyan Ubangiji.”


Sai ta amsa masa, “Ka yi mini alheri, da yake ka tura ni a ƙasar Negeb, ka ba ni maɓuɓɓugan ruwa.” Kalibu kuwa ya ba ta maɓuɓɓugan tuddai da na kwari.


Ta kuwa ce masa, “Ka yi mini alheri, da yake ka tura ni a ƙasar Negeb, ina roƙonka ka ba ni maɓuɓɓugar ruwa.” Kalibu kuwa ya ba ta maɓuɓɓugar tuddai da na kwari.


Yakubu ya ce, “A'a, ina roƙonka, in dai na sami tagomashi a idonka, to, sai ka karɓi kyautar da yake hannuna, gama hakika ganin fuskarka, kamar ganin fuskar Allah ne, bisa ga yadda ka karɓe ni.


Sa'an nan Isuwa ya ce, “Bari mu ci gaba da tafiyarmu, ni kuwa in wuce gabanka.”


Saboda haka kyautar ta yi gaba, shi kansa kuwa a daren, ya sauka a zango.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ