27 Sai ya ce masa, “Yaya sunanka?” Ya ce, “Yakubu.”
27 Mutumin ya tambaye shi ya ce, “Mene ne sunanka?” Yaƙub ya amsa ya ce, “Yaƙub.”
Sa'an nan sai mutumin ya ce, “Ka bar ni in tafi, gama gari na wayewa.” Amma Yakubu ya ce, “Ba zan bar ka ka tafi ba, sai ka sa mini albarka.”
Sai ya ce, “Ba za a ƙara kiranka da suna Yakubu ba, amma za a kira ka Isra'ila, gama ka yi kokawa da Allah da mutane, ka kuwa yi rinjaye.”
Allah kuwa ya ce masa, “Sunanka Yakubu ne, amma nan gaba ba za a ƙara kiran sunanka Yakubu ba, sai Isra'ila.” Don haka aka kira sunansa Isra'ila.
Sai macen ta ce, “Na rantse da Ubangiji da kai kuma, ba zan bar ka ba.” Sai Elisha ya tashi, ya bi ta.
Yabez ya roƙi Allah na Isra'ila, ya ce, “Ka sa mini albarka, ka faɗaɗa kan iyakata, hannunka kuma ya kasance tare da ni, ka kuma kiyaye ni daga abin da zai cuce ni.” Allah kuwa ya biya masa bukatarsa.
Ubangiji ya amsa maka a ranar wahala! Allah na Yakubu ya kiyaye ka!
Kakanmu Yakubu ya gudu zuwa ƙasar Aram, A can Isra'ila ya yi barantaka saboda mace, Saboda mace ya yi kiwon tumaki.