47 Laban ya sa masa suna Yegar-sahaduta, amma Yakubu ya kira shi Galeyed.
47 Laban ya sa masa suna Yegar Sahaduta, Yaƙub kuwa ya kira shi Galeyed.
Saboda haka, tun da taron shaidu masu ɗumbun yawa suka kewaye mu haka, sai mu ma mu yar da dukkan abin da ya nauyaya mana, da kuma zunubin da ya ɗafe mana, mu kuma yi tseren nan da yake gabanmu tare da jimiri,
Yakubu ya ce wa iyalinsa, “Ku tattara duwatsu.” Sai suka ɗauki duwatsu, suka tsiba, suka kuwa ci abinci kusa da tsibin.
Ra'ubainawa da Gadawa suka sa wa bagaden suna Shaida, domin in ji su, “Shi shaida ne a tsakaninmu, cewa Ubangiji shi ne Allah.”
Sa'an nan suka zo Gileyad da Kadesh cikin ƙasar Hittiyawa, daga nan suka tafi Dan-ja'an. Daga Dan-ja'an kuma suka ratsa zuwa Sidon.