20 Yakubu kuwa ya yaudari Laban Ba'aramiye da bai sanar da shi zai gudu ba.
20 Yaƙub kuwa ya ruɗe Laban mutumin Aram da bai sanar da shi zai gudu ba.
Ishaku yana da shekara arba'in sa'ad da ya auri Rifkatu, 'yar Betuwel Ba'aramiye daga Fadan-aram 'yar'uwar Laban Ba'aramiye.
Amma a sa'an nan Laban ya riga ya tafi ya yi wa tumakinsa sausaya, sai Rahila ta sace gumakan gidan mahaifinta.
Ya gudu da dukan abin da yake da shi, ya tashi ya haye Yufiretis, ya miƙe zuwa ƙasar Gileyad ta tuddai.
Me ya sa ka gudu a ɓoye? Ka cuce ni, ba ka kuwa faɗa mini ba, ai, da na sallame ka da farin ciki, da waƙe-waƙe, da kiɗa, da garaya.
Sa'an nan kuma sai ku hurta waɗannan kalmomi a gaban Ubangiji Allahnku, ku ce, ‘Ubana Ba'aramiye ne, mayawaci a dā. Ya gangara zuwa Masar yana da jama'a kima, ya yi baƙunci a wurin. Amma a can ya zama al'umma mai girma, mai iko, mai yawa.