Sai Nebukadnezzar ya husata ƙwarai da Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, har fuskarsa ta sāke. Sai ya umarta a ƙara zuga wutar, har sau bakwai fiye da yadda take a dā.
Wannan shi ne tanadi domin wanda ya yi kisankai, wato wanda zai gudu zuwa can don ya tsira. Idan ya kashe abokinsa ba da niyya ba, ba kuma ƙiyayya a tsakaninsu a dā,
Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangijina, ni ba mai lafazi ba ne, ban taɓa zama ba, ko a yanzu ma, bayan da ka yi magana da bawanka, gama ni mai nauyin baki ne, mai nauyin harshe kuma.”
Yakubu ya ji 'ya'yan Laban suna cewa, “Yakubu ya kwashe dukan abin da yake na mahaifinmu, daga cikin dukan abin da yake na mahaifinmu kuma ya sami dukiyarsa.”