Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 30:32 - Littafi Mai Tsarki

32 bar ni, in ratsa garkenka duka yau, in keɓe dukan masu dabbare-dabbare da tumaki babare-babare, da kowane ɗan rago baƙi, da dabbare-dabbare da babare-babare na awaki, waɗannan ne za su zama ladana.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

32 Bari in ratsa cikin dukan garkunanka yau in fid da masu dabbare-dabbare da tumaki babare-babare, da kowane ɗan rago baƙi, da dabbare-dabbare da babare-babare na awaki daga ciki, waɗannan ne za su zama ladana.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 30:32
5 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

In ya ce, ‘Dabbare-dabbare, su ne ladanka,’ duk garken sai ya haifi dabbare-dabbare, in kuma ya ce ‘masu sofane ne ladanka,’ sai garken duka ya haifi masu sofane.


“A lokacin ɗaukar cikin garke, cikin mafarki na ta da idanuna, na kuwa gani cikin mafarkin, bunsuran da suke hawan garken, masu sofane, da dabbare-dabbare da roɗi-roɗi ne.


Amma a ran nan Laban ya ware bunsuran da suke dabbare-dabbare da masu sofane, da dukan awakin da suke dabbare-dabbare da kyalloli, da dukan baƙaƙen tumaki, ya danƙa su a hannun 'ya'yansa maza,


Ya ce, “Me zan ba ka?” Yakubu ya ce, “Ba za ka ba ni kome ba, in da za ka yi mini wannan, sai in sāke kiwon garkenka in lura da shi,


Ta haka amincina zai shaide ni a gabanka a sa'ad da ka zo bincike hakkina. Duk wanda aka iske ba dabbare-dabbare ba ne, kuma ba babare-babare ba ne cikin awaki, ba kuma baƙi ba ne a cikin raguna, in aka samu a wurina, sai a ɗauka, na sata ne.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ