22 Allah kuwa ya tuna da Rahila, ya saurare ta, ya buɗe mahaifarta.
22 Sai Allah ya tuna da Rahila; ya saurare ta ya kuma buɗe mahaifarta.
Sa'ad da Ubangiji ya ga ana ƙin Lai'atu, ya buɗe mahaifarta, amma Rahila bakarariya ce.
Allah kuwa ya tuna da Nuhu da dukan dabbobin gida da na jeji waɗanda suke cikin jirgi tare da shi. Allah ya sa iska ta hura bisa duniya, ruwaye suka janye.
Yakan girmama matar da ba ta haihuwa a gidanta, Yakan sa ta yi farin ciki ta wurin ba ta 'ya'ya. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
Fushin Yakubu ya yi ƙuna a kan Rahila, ya ce, “Ina daidai da Allah ne, wanda ya hana ki haihuwa?.”
'Ya'ya kyauta ne daga wurin Ubangiji, Albarka ce ta musamman.
Ya tuna da alkawarinsa mai tsarki Wanda ya yi wa bawansa Ibrahim.
Ishaku kuwa ya yi addu'a sai matarsa Rifkatu ta yi ciki.
Daga baya ta haifi 'ya mace, ta kuwa raɗa mata suna Dinatu.
'Ya'yan Rahila, su ne Yusufu da Biliyaminu.