(waɗannan su ne 'ya'yan Lai'atu, maza, waɗanda ta haifa wa Yakubu cikin Fadan-aram, da 'ya tasa kuma Dinatu, 'ya'yansa mata da maza duka, mutum talatin da uku ne).
Sai Lai'atu ta ce, “Allah ya wadata ni da kyakkyawar baiwa, yanzu mijina zai darajanta ni, domin na haifa masa 'ya'ya maza shida,” ta raɗa masa suna Zabaluna.