Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 30:15 - Littafi Mai Tsarki

15 Amma ta ce mata, “Kanƙanen abu ne da kika ƙwace mini mijina? Za ki kuma ƙwace manta uwar da ɗana ya samo kuma?” Rahila ta ce, “To, in haka ne, bari ya kwana tare da ke a daren yau a maimakon manta uwar da ɗanki ya samo.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 Amma ta ce mata, “Bai ishe ki ba ne da kika ƙwace mijina? Yanzu kuma kina so ki ƙwace manta-uwa na yarona?” Sai Rahila ta ce “Shi ke nan, mijina zai iya kwana da ke yau saboda manta-uwa na ɗanki.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 30:15
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kana jin ƙaramin abu ne da ka fitar da mu daga cikin ƙasar mai yalwar abinci, don ka kashe mu a jeji? So kake kuma ka mai da kanka sarki a bisanmu?


A gare ni kam, sassauƙan abu ne a ce ku ne za ku gwada ni, ko kuwa a gwada ni a gaban kowace mahukunta ta mutane. Ni ma ba na gwada kaina.


Ba ki bi hanyoyinsu da abubuwansu na banƙyama kaɗai ba, sai ka ce wannan ya yi miki kaɗan, amma kin lalace fiye da su.


Ga amsar da Ishaya ya ba Ahaz, “Kasa kunne yanzu, kai zuriyar sarki Dawuda. Ba abin kirki kuke yi ba, da kuka ƙure haƙurin jama'a, haƙurin Allah kuma kuke so ku ƙure?


A kwanakin kakar alkama, Ra'ubainu ya fita ya samo manta uwa a saura, ya kawo wa mahaifiyarsa Lai'atu. Sai Rahila ta ce wa Lai'atu, “Ina roƙonki, ɗiba mini daga cikin manta uwar da ɗanki ya samo.”


Sa'ad da Yakubu ya komo daga saura da maraice, Lai'atu ta fita ta tarye shi, ta ce, “Sai ka shigo wurina, gama na riga na ijarar da kai da manta uwar da ɗana ya samo.” Saboda haka ya kwana tare da ita a daren nan.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ