Amma ina tsoro kada yă zamana, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa'u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Almasihu.
Ku na ubanku Iblis ne, niyyarku kuwa ku aikata burin ubanku. Shi dā ma tun farko mai kisankai ne, bai zauna kan gaskiya ba, don ba ruwansa da gaskiya. Duk sa'ad da yake ƙarya, cinikinsa yake yi, don shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.
Ya ce wa sarki, “Ubangiji ya ce, ‘Domin ka aiki manzanni su yi tambaya wurin Ba'alzabul, gunkin Ekron, ba Allah a Isra'ila ne wanda za ka yi tambaya a wurinsa? Domin haka ba za ka sauko daga kan gadon da kake kwance ba, amma za ka mutu lalle.’ ”
Suka ce masa, “Wani mutum ya sadu da mu, ya ce mana, mu koma wurinka mu shaida maka, ‘Ubangiji ya ce, ba Allah a Isra'ila, har aka aike ku ku tambayi Ba'alzabul, gunkin Ekron? Domin haka ba za ka tashi daga kan gadon da kake kwance ba, amma lalle za ka mutu.’ ”
Ku faɗa wa sarki, Ubangiji ya ce, ‘Ba za ka tashi daga kan gadon da kake kwance ba, amma lalle za ka mutu.’ ” Iliya ya yi kamar yadda Ubangiji ya umarce shi, sai ya tafi.
Idan wani mutum ya ji zantuttukan la'anan nan sa'an nan ya sa wa kansa albarka a zuciyarsa, yana cewa, ‘Ba abin da zai same ni ko na bi taurin zuciyata,’ wannan zai haddasa lalacewar ɗanye da busasshe gaba ɗaya.
Sai ya ce, ‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakin dukan annabawansa.’ Sa'an nan Ubangiji ya ce, ‘To, za ka ruɗe shi har ka yi nasara. Je ka, ka yi haka nan.’