Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 3:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Sa'an nan Ubangiji Allah ya ce, “Ga shi, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san nagarta da mugunta, yanzu fa, kada ya miƙa hannunsa ya ɗiba daga cikin itacen rai ɗin nan, ya ci, ya rayu har abada.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Ubangiji Allah ya kuma ce, “To, fa, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu. Kada a yarda yă miƙa hannunsa yă ɗiba daga itacen rai yă ci, yă kuma rayu har abada.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 3:22
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi izinin cin 'ya'yan itacen rai, wanda yake a cikin Firdausin Allah.’ ”


Albarka tā tabbata ga masu wanke rigunansu, domin su sami izinin ɗiba daga itacen rai, su kuma shiga birnin ta ƙofa.


ta tsakiyar hanyar birnin kuma, ta kowane gefen kogin, akwai itatuwan rai masu haihuwar 'ya'ya iri goma sha biyu, kowane wata suna haihuwa, ganyen itatuwan kuwa saboda lafiyar al'ummai ne.


Masu farin ciki ne waɗanda suka sami hikima, hikima za ta ba su rai kamar yadda itace yakan ba da 'ya'ya.


Ubangiji Allah ya sa kowane itace mai kyan gani, mai amfani domin abinci, ya tsiro, itacen rai kuwa yana tsakiyar gonar, da kuma itacen sanin nagarta da mugunta.(Far 3.22,24; W. Yah 2.7; 22.2,14,19; Eze 47.12.)


Allah kuma ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, da kamanninmu, su mallaki kifayen da suke a cikin teku, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobi, da dukan duniya, da kowane abu mai rarrafe da yake rarrafe bisa ƙasa.”


Gama Allah ya sani a ranar da kuka ci daga itacen nan idanunku za su buɗe, za ku kuwa zama kamar Allah, ku san nagarta da mugunta.”


Ya ku mazaunan Lebanon, Waɗanda suke zaune cikin itatuwan al'ul, Irin nishin da za ku yi sa'ad da azaba ta same ku, Azaba ce irin ta mace mai naƙuda!


Matalauta za su ci yadda suke so, Masu zuwa wurin Ubangiji za su yabe shi, Su arzuta har abada!


Ubangiji Allah kuwa ya yi wa mutumin da matarsa tufafi na fata, ya suturce su.


Domin haka Ubangiji Allah ya fisshe shi daga cikin gonar Aidan, ya noma ƙasa, wato inda aka ɗauko shi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ