ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya ne suke girma a ƙasar jama'ata. Ku yi kuka domin dukan gidajen da mutane suke murna a cikinsu dā, domin kuma birnin da yake cike da jin daɗi a dā.
Zan bar ciyayi su rufe ta. Ba zan yi wa kurangar inabin aski ba, ko in yi mata noma, amma zan bar sarƙaƙƙiya da ƙayayuwa su rufe ta. Har ma zan sa gizagizai su hana ta ruwan sama.”
to, sai ku tabbata Ubangiji Allahnku ba zai dinga korar al'umman nan daga gabanku ba, za su zama muku azargiya, da tarko, da bulala a kwiyaɓunku, da ƙayayuwa a idanunku. Da haka za ku ƙare sarai daga cikin kyakkyawar ƙasan nan da Ubangiji Allahnku ya ba ku.
Sun shuka alkama, sun girbe ƙayayuwa, Sun gajiyar da kansu, amma ba su amfana da kome ba. Za su sha kunya saboda abin da suke girbe, Saboda zafin fushin Ubangiji.”
Ga Adamu kuwa ya ce, “Ka kasa kunne ga muryar matarka, har ka ci daga 'ya'yan itacen da na dokace ka, ‘Kada ka ci daga cikinsu.’ Tun da ka aikata wannan za a la'antar da ƙasa saboda kai, da wahala za ka ci daga cikinta muddin rayuwarka.
Za ka yi zuffa da aiki tuƙuru kafin ka sami abinci, har ka koma ƙasa, gama da ita aka siffata ka, kai turɓaya ne, ga turɓaya kuma za ka koma.” (2Tas 3.10; Far 2.7; Zab 90.3; 104.29; M.Had 12.7)