Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 3:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Maciji ya fi kowace dabba da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa matar, “Ko Allah ya ce, ‘Ba za ku ci daga wani itacen da yake a gonar ba?’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 To, maciji dai ya fi kowane a cikin namun jejin da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa macen, “Tabbatacce ne Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga kowane itace a lambu’?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 3:1
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma ina tsoro kada yă zamana, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa'u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Almasihu.


Ba abin mamaki ba ne kuwa, domin ko Shaiɗan ma da kansa, yakan mai da kansa kamar shi mala'ikan haske ne.


Sai aka jefa ƙaton macijin nan a ƙasa, wato macijin nan na tun dā dā, wanda ake kira Ibilis da Shaiɗan, mayaudarin dukkan duniya, aka jefa shi a duniya, mala'ikunsa ma aka jefa su tare da shi.


Sai ya kama macijin nan, wato, macijin nan na tun dā dā, wanda yake shi ne Ibilis, shi ne kuma Shaiɗan, ya ɗaure shi har shekara dubu,


Sai Mai Gwadawar nan ya zo, ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama gurasa.”


“Ga shi, na aike ku kamar tumaki a tsakiyar kyarketai. Don haka sai ku zama masu azanci kamar macizai, da kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi.


ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, to dira ƙasa. Don a rubuce yake cewa, ‘Zai yi wa mala'ikunsa umarni game da kai,’ da kuma ‘Za su tallafe ka, Don kada ka yi tuntuɓe da dutse.’ ”


A wannan rana Ubangiji zai yi amfani da takobinsa mai ƙarfi, mai muguwar ɓarna, don ya hukunta dodon ruwan nan mai kanannaɗewa, mai murɗewa, ya kashe dodon da yake cikin teku.


Gama idan ɗaya daga cikinsu ya fāɗi, ɗayan zai taimake shi ya tashi, amma idan ya faɗi yana shi kaɗai, to, tir, domin ba wanda zai taimake shi.


Ya kuma ce masa, “Duk waɗannan zan ba ka in ka faɗi a gabana ka yi mini sujada.”


Haka kuma, ku maza, ku yi zaman ɗa'a da matanku, kuna girmama su, da yake su ne raunana, gama ku abokan tarayya ne na Allah. Ku yi haka don kada wani abu ya hana ku yin addu'a tare.


Sai macijin ya kwarara ruwa daga bakinsa kamar kogi daga bayan matar, don ya share ta da ambaliya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ