Bal'amu kuwa ya faɗi jawabinsa, ya ce “Tun daga Aram Balak ya kawo ni, Shi Sarkin Mowab ne daga gabashin duwatsu. ‘Zo, la'anta mini Yakubu, Zo, ka tsine wa Isra'ila!’
Madayanawa, da Amalekawa, da mutanen gabas duka suna nan da yawa a shimfiɗe cikin kwarin, kamar fara. Raƙumansu kuma suna da yawa kamar yashi a bakin teku. Ba wanda zai iya ƙidaya su.
Baran ya ɗibi raƙuma goma daga cikin raƙuman maigidansa. Ya tashi, yana ɗauke da tsaraba ta kowane irin abu mai kyau na maigidansa a hannunsa. Ya kama hanyar Mesofotamiya zuwa birnin Nahor.
Allah ya ce wa Yakubu, “Tashi, ka hau zuwa Betel, ka zauna can. Can za ka gina bagade ga Allah wanda ya bayyana gare ka sa'ad da kake guje wa ɗan'uwanka Isuwa.”