Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 28:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Yakubu ya yi wa'adi da cewa, “Idan Allah zai kasance tare da ni, ya kiyaye ni cikin tafiyan nan da nake yi, ya kuma ba ni abincin da zan ci, da suturar da zan sa,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Sa’an nan Yaƙub ya yi alkawari cewa, “In Allah zai kasance tare da ni yă kuma lura da ni a wannan tafiya, yă kuma ba ni abinci in ci da tufafi in sa,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 28:20
29 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

To, in muna da abinci da sutura, ai, sai mu dangana da su.


Gama na yi wa'adi sa'ad da nake zaune a Geshur ta Suriya. Na yi wa'adi cewa, ‘Idan dai Ubangiji ya komar da ni Urushalima zan bauta masa.’ ”


Dukanmu kuwa daga falala tasa muka samu, alheri kan alheri.


Zan kawo hadayun ƙonawa a ɗakinka, Zan miƙa maka abin da na alkawarta.


Ni ne Allah na Betel, inda ka zuba wa dutsen mai, ka kafa shi al'amudi, ka kuma rantse mini. Yanzu fa tashi ka fita daga cikin ƙasan nan, ka koma ƙasar haihuwarka.’ ”


Bulus kuwa da ya ƙara kwanaki da yawa, bayan ya sausaye kansa a Kankiriya don ya cika wa'adin da ya ɗauka, ya yi bankwana da 'yan'uwa, ya shiga jirgin ruwa zuwa ƙasar Suriya, tare da Bilikisu da Akila.


Ka tuna, ya Ubangiji, da alkawarin da ya yi, Da rantsuwar da ya yi maka, ya Maɗaukaki, Allah na Isra'ila,


Zan cika muhimmin alkawarina, In yi biyayya da koyarwarka mai adalci.


A taron dukan jama'arka, A shirayun Haikalinka, A Urushalima, zan ba ka abin da na alkawarta. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!


Zan ba shi abin da na alkawarta A taron dukan jama'arsa.


Ku ba Ubangiji Allahnku abin da kuka alkawarta masa, Dukanku sauran al'umma da kuke kusa, ku kawo masa kyautai. Allah yakan sa mutane su ji tsoronsa,


Don haka zan yi ta raira waƙar yabonka kullayaumin, A sa'ad da nake miƙa maka abin da na alkawarta.


Ya Allah, kā ji alkawaraina, Kā kuwa ba ni abin da ya dace, Tare da waɗanda suke ɗaukaka ka.


Zan miƙa maka abin da na yi alkawari, ya Allah, Zan miƙa maka hadaya ta godiya.


Ubangiji zai bayyana kansa ga mutanen Masar, sa'ad da ya yi haka kuwa, za su karɓe shi, su yi masa sujada, su kuma kawo masa hadayu da sadakoki. Za su yi masa alkawarai ƙwarara, su kuwa cika abin da suka alkawarta.


Zan yabe ka a gaban babban taron jama'a Saboda abin da ka yi, A gaban dukan masu yi maka biyayya, Zan miƙa sadakokin da na alkawarta.


A ran nan kuwa Isra'ilawa sun sha wahala, gama Saul ya yi rantsuwa mai ƙarfi ya ce, “La'ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin faɗuwar rana tun ban ɗauko fansa a kan abokan gābana ba.” Don haka ba mutumin da ya ɗanɗana abinci.


Saboda haka nake miƙa shi ga Ubangiji muddin ransa. Ya zama na Ubangiji.” A can ya yi wa Ubangiji sujada.


Ta yi wa'adi, ta ce, “Ya Ubangiji Mai Runduna, idan lalle ka dube ni, ni baiwarka, ka tuna da ni, ba ka manta da ni baiwarka ba, amma ka ba ni ɗa, ni ma sai in ba da shi ga Ubangiji dukan kwanakinsa, aska kuwa ba za ta taɓa kansa ba.”


Ga shi, ina tare da kai, zan kiyaye ka duk inda ka tafi, zan kuwa komo da kai ƙasan nan, gama ba zan rabu da kai ba, sai na aikata abin nan da na hurta maka.”


sa'an nan mu tashi mu haura zuwa Betel, domin in kafa bagade ga Allah wanda ya taimake ni a kwanakin ƙuncina, wanda kuwa yake tare da ni duk inda na tafi.”


Yabez ya roƙi Allah na Isra'ila, ya ce, “Ka sa mini albarka, ka faɗaɗa kan iyakata, hannunka kuma ya kasance tare da ni, ka kuma kiyaye ni daga abin da zai cuce ni.” Allah kuwa ya biya masa bukatarsa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ