Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 28:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Tashi, ka tafi Fadan-aram, zuwa gidan Betuwel kakanka na wajen uwa, ka zaɓo wa kanka mata daga cikin 'ya'ya mata na Laban ɗan'uwan mahaifiyarka a can.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Tashi nan da nan ka tafi Faddan Aram, zuwa gidan mahaifin mahaifiyarka Betuwel. Ka ɗauko wa kanka mata a can daga cikin ’ya’ya matan Laban ɗan’uwan mahaifiyarka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 28:2
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ishaku yana da shekara arba'in sa'ad da ya auri Rifkatu, 'yar Betuwel Ba'aramiye daga Fadan-aram 'yar'uwar Laban Ba'aramiye.


Kakanmu Yakubu ya gudu zuwa ƙasar Aram, A can Isra'ila ya yi barantaka saboda mace, Saboda mace ya yi kiwon tumaki.


(waɗannan su ne 'ya'yan Lai'atu, maza, waɗanda ta haifa wa Yakubu cikin Fadan-aram, da 'ya tasa kuma Dinatu, 'ya'yansa mata da maza duka, mutum talatin da uku ne).


Allah kuma ya sāke bayyana ga Yakubu a lokacin da ya komo daga Fadan-aram, ya sa masa albarka.


ban cancanci ayyukanka na ƙauna da irin amincin da ka gwada wa baranka ba, gama da sandana kaɗai na haye Kogin Urdun, ga shi yanzu kuwa na zama ƙungiya biyu.


Da haka, Ishaku ya sallami Yakubu, ya kuwa tafi Fadan-aram wurin Laban, ɗan Betuwel Ba'aramiye ɗan'uwan Rifkatu, mahaifiyar Yakubu da Isuwa.


Laban da Betuwel suka amsa suka ce, “Wannan al'amari daga Ubangiji ne, ba mu da iko mu ce maka i, ko a'a.


Rifkatu kuwa tana da ɗan'uwa sunansa Laban. Sai Laban ya sheƙo zuwa wurin mutumin a bakin rijiya.


Baran ya ɗibi raƙuma goma daga cikin raƙuman maigidansa. Ya tashi, yana ɗauke da tsaraba ta kowane irin abu mai kyau na maigidansa a hannunsa. Ya kama hanyar Mesofotamiya zuwa birnin Nahor.


ya kora shanunsa duka, da dukan bisashen da ya samu, da shanu da suke nasa, waɗanda ya samu a Fadan-aram a ƙasar Mesofotamiya, zuwa ƙasar Kan'ana wurin mahaifinsa Ishaku.


Yakubu kuwa ya ci gaba da tafiyarsa, har ya kai ƙasar Mesofotamiya.


Yakubu kuwa ya kai birnin Shalem wanda yake ƙasar Kan'ana lafiya, a kan hanyarsa daga Fadan-aram, ya kuwa yi zango a ƙofar birnin.


Amma za ka tafi ƙasata, daga cikin dangina ka auro wa ɗana Ishaku mata.”


Ta wurin annabi Ubangiji ya fito da mutanen Isra'ila daga Masar, Ta wurin annabi kuma ya kiyaye su.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ