Allah ya ce wa Yakubu, “Tashi, ka hau zuwa Betel, ka zauna can. Can za ka gina bagade ga Allah wanda ya bayyana gare ka sa'ad da kake guje wa ɗan'uwanka Isuwa.”
“Ko da yake mutanen Isra'ila suna karuwanci, Kada kuma mutanen Yahuza su yi laifi. Kada ku tafi Gilgal, Ko ku haura zuwa Bet-awen. Kada ku yi rantsuwa da cewa, ‘Har da zatin Ubangiji!’
Ya zakuɗa daga nan zuwa dutsen da yake gabashin Betel, ya kafa alfarwarsa, Betel tana yamma, Ai tana gabas, a nan ya gina wa Ubangiji bagade, ya kira bisa sunan Ubangiji.
Da ya isa wani wuri, sai ya kwana can a wannan dare, don rana ta riga ta faɗi. Ya ɗauki ɗaya daga cikin duwatsun da suke wurin, ya yi matashin kai da shi, ya kwanta, ya yi barci.
Ni ne Allah na Betel, inda ka zuba wa dutsen mai, ka kafa shi al'amudi, ka kuma rantse mini. Yanzu fa tashi ka fita daga cikin ƙasan nan, ka koma ƙasar haihuwarka.’ ”
Sa'ad da ka wuce nan, ka ci gaba zuwa itacen oak a Tabor, a nan mutum uku da suke haurawa zuwa ɗakin Allah a Betel za su gamu da kai. Ɗaya yana ɗauke da 'yan awaki uku, ɗaya kuma yana ɗauke da malmalar abinci guda uku, ɗayan kuwa yana ɗauke da salkar ruwan inabi.
Dukan rundunan Isra'ilawa suka haura zuwa Betel, suka yi makoki, suka zauna a gaban Ubangiji suka yi azumi har maraice. Sa'an nan suka miƙa wa Ubangiji hadayu na ƙonawa da na salama.
Sai Iliya ya ce wa Elisha, “Ina roƙonka, ka dakata a nan, gama Ubangiji ya aike ni har zuwa Betel.” Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji da kuma kai kanka, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka tafi Betel.
Abaija ya runtumi Yerobowam, ya ƙwace masa waɗansu birane, wato Betel tare da ƙauyukanta, da Yeshana tare da ƙauyukanta, da kuma Efron tare da ƙauyukanta.