Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 28:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Ga shi kuwa, Ubangiji na tsaye a kansa yana cewa, “Ni ne Ubangiji, Allah na Ibrahim, mahaifinka, da Ishaku, ƙasar da kake kwance a kai, zan ba ka ita da zuriyarka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 A can bisanta Ubangiji ya tsaya, ya kuma ce, “Ni ne Ubangiji Allah na mahaifinka Ibrahim da kuma Allah na Ishaku. Zan ba ka, kai da kuma zuriyarka, ƙasar da kake kwance a kai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 28:13
40 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

gama dukan ƙasan nan da kake gani kai zan ba, da zuriyarka har abada.


Yakubu ya ce wa Yusufu, “Allah Maɗaukaki ya bayyana gare ni a Luz a ƙasar Kan'ana ya sa mini albarka,


Na ba ka ƙasar da na ba Ibrahim da Ishaku, zan kuma ba da ita ga zuriyarka a bayanka.”


Da daren nan Ubangiji ya bayyana gare shi ya ce, “Ni ne Allah na mahaifinka, kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai, zan sa maka albarka in riɓaɓɓanya zuriyarka saboda bawana Ibrahim.”


Sai Ubangiji ya bayyana ga Abram, ya ce, “Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa.” Sai ya gina bagade ga Ubangiji, wanda ya bayyana gare shi.


Allah ya ce wa Yakubu, “Tashi, ka hau zuwa Betel, ka zauna can. Can za ka gina bagade ga Allah wanda ya bayyana gare ka sa'ad da kake guje wa ɗan'uwanka Isuwa.”


Amma bisa ga hakika sun ɗokanta ne a kan wata ƙasa mafi kyau, wato ta Sama. Saboda haka ne, Allah ba ya jin kunya a ce da shi Allahnsu, don kuwa ya shirya musu birni.


Ya kuma ce, “Ni ne Allah na kakanninka, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.” Sai Musa ya ɓoye fuskarsa, gama yana jin tsoro ya dubi Allah.


‘Ni ne Allahn Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.’ Ai, waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba.”


Sai ya ce, “Ni ne Allah, Allah na mahaifinka, kada ka ji tsoron zuwa Masar, gama a can zan maishe ka babbar al'umma.


Sa'ad da take cikin naƙudarta, sai ungozoma ta ce mata, “Kada ki ji tsoro, gama yanzu kin sami wani ɗa.”


Sai Yakubu ya ce, “Ya Allah na kakana Ibrahim, da mahaifina Ishaku, Ubangiji, wanda ka ce mini, ‘Koma ƙasarka zuwa wurin danginka, zan kuwa yi maka alheri,’


Da ba domin Allah na mahaifina da Ibrahim, da martabar Ishaku na wajena ba, hakika da yanzu ka sallame ni hannu wofi. Allah ya ga wahalata da aikin hannuwana, ya kuwa tsauta maka a daren jiya.”


ya kuma sa ka sami albarkar Ibrahim da zuriyarka tare da kai, har da za ka amshe ƙasar baƙuncinka wadda Allah ya bai wa Ibrahim!”


Ka yi baƙunci cikin wannan ƙasa, ni kuwa zan kasance tare da kai, zan sa maka albarka, gama a gare ka da zuriyarka ne na ba da waɗannan ƙasashe, zan kuwa cika rantsuwar da na yi wa Ibrahim mahaifinka.


Bayan waɗannan al'amura, maganar Ubangiji ta zo ga Abram cikin wahayi cewa, “Abram, kada ka ji tsoro, ni ne garkuwarka, kana da lada mai yawa.”


Amma kuwa shi kansa, bai ba shi gādonta ba, ko da taki ɗaya, sai dai ya yi masa alkawari zai mallakar masa ita, shi da zuriyar bayansa, ko da yake ba shi da ɗa a lokacin.


“Zan ba ka ƙasar Kan'ana, Za ta zama mallakarka.”


Yakubu ya kira sunan wurin da Allah ya yi magana da shi, Betel.


Tashi, ka yi tafiya cikin ratar ƙasar da fāɗinta, gama zan ba ka ita.”


A wannan rana Ubangiji ya yi wa Abram alkawari ya ce, “Ga zuriyarka na ba da wannan ƙasa, daga Kogin Masar zuwa babban kogi, wato Kogin Yufiretis ke nan,


ya ce musu, “Na ga ba ni da sauran farin jini wurin mahaifinku kamar dā. Amma Allah na mahaifina yana tare da ni.


Ni ne Allah na Betel, inda ka zuba wa dutsen mai, ka kafa shi al'amudi, ka kuma rantse mini. Yanzu fa tashi ka fita daga cikin ƙasan nan, ka koma ƙasar haihuwarka.’ ”


Allah na Ibrahim da Nahor, Allah na mahaifinsu, ya shara'anta tsakaninmu.” Saboda haka Yakubu ya rantse da martabar mahaifinsa Ishaku.


Allah kuwa ya ji nishinsu, sai ya tuna da alkawarinsa da ya yi wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.


Sai Ubangiji ya ce, “Ta haka za su gaskata Ubangiji Allah na kakanninsu ne, wato na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, ya bayyana gare ka.”


Na kuma yi musu alkawari zan ba su ƙasar Kan'ana, inda suka yi zaman baƙunci.


Duba, na sa ƙasar a gabanku, sai ku shiga ku mallake ta, ƙasa wadda na rantse wa kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, cewa zan ba su, su da zuriyarsu a bayansu.’ ”


Ba saboda adalcinku, ko kuma gaskiyarku ne ya sa za ku shiga ƙasar, ku mallake ta ba, amma saboda muguntar waɗannan al'ummai ne, Ubangiji Allahnku ya kore su a gabanku domin kuma ya cika maganar da ya rantse wa kakanninku, wato su Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.


Ubangiji ya ce masa, “Wannan ita ce ƙasar da na rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, zan ba da ita ga zuriyarsu. Na bar ka ka gan ta da idanunka, amma ba za ka haye, ka shiga ba.”


Ubangiji kuma ya nuna mini wani wahayi. A wahayin sai na gan shi, yana tsaye kusa da bangon da ake ginawa. Yana riƙe da igiyar awon gini.


ban cancanci ayyukanka na ƙauna da irin amincin da ka gwada wa baranka ba, gama da sandana kaɗai na haye Kogin Urdun, ga shi yanzu kuwa na zama ƙungiya biyu.


Zan tallafe ku, ku zama jama'ata, ni kuwa in zama Allahnku. A sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya 'yanto ku daga wulakancin Masarawa.


Yarjejeniyar da ya yi da Ibrahim, Da alkawarin da ya yi wa Ishaku.


“Zan ba ka ƙasar Kan'ana, Za ta zama mallakarka.”


“Ubangiji Allah ya ce, ‘Sa'ad da na tattara mutanen Isra'ila daga cikin sauran al'umma, inda na watsar da su, na kuma bayyana tsarkina a cikinsu a kan idon al'ummai, sa'an nan za su zauna a ƙarsarsu wadda na ba bawana Yakubu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ